Sura Ad-Dhuhaa — The Morning Hours

Sura Ad-Dhuhaa (The Morning Hours) — 93/114 · 11 aya. Karanta kuma ka saurara da rubutun Larabci da fassarar Hausa.

وَٱلضُّحَىٰ

Inã rantsuwa da hantsi

Ayah 1

وَٱلَّيۡلِ إِذَا سَجَىٰ

Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa)

Ayah 2

مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ

Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba

Ayah 3

وَلَلۡأٓخِرَةُ خَيۡرࣱ لَّكَ مِنَ ٱلۡأُولَىٰ

Kuma lalle ta ƙarshe* ce mafi alheri a gare ka daga ta farko

Ayah 4

وَلَسَوۡفَ يُعۡطِيكَ رَبُّكَ فَتَرۡضَىٰٓ

Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda

Ayah 5

أَلَمۡ يَجِدۡكَ يَتِيمࣰ ا فَـَٔاوَىٰ

Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma

Ayah 6

وَوَجَدَكَ ضَآلࣰّ ا فَهَدَىٰ

Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai

Ayah 7

وَوَجَدَكَ عَآئِلࣰ ا فَأَغۡنَىٰ

Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka

Ayah 8

فَأَمَّا ٱلۡيَتِيمَ فَلَا تَقۡهَرۡ

Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi

Ayah 9

وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنۡهَرۡ

Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa

Ayah 10

وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ

Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya)

Ayah 11