Sura Al-Aadiyaat — The Chargers

Sura Al-Aadiyaat (The Chargers) — 100/114 · 11 aya. Karanta kuma ka saurara da rubutun Larabci da fassarar Hausa.

وَٱلۡعَٰدِيَٰتِ ضَبۡحࣰ ا

Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki

Ayah 1

فَٱلۡمُورِيَٰتِ قَدۡحࣰ ا

Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa

Ayah 2

فَٱلۡمُغِيرَٰتِ صُبۡحࣰ ا

Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba

Ayah 3

فَأَثَرۡنَ بِهِۦ نَقۡعࣰ ا

Sai su motsar da ƙũra game da shi

Ayah 4

فَوَسَطۡنَ بِهِۦ جَمۡعًا

Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya

Ayah 5

إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودࣱ‏

Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa

Ayah 6

وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدࣱ‏

Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka

Ayah 7

وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلۡخَيۡرِ لَشَدِيدٌ

Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne

Ayah 8

۞أَفَلَا يَعۡلَمُ إِذَا بُعۡثِرَ مَا فِي ٱلۡقُبُورِ

Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura

Ayah 9

وَحُصِّلَ مَا فِي ٱلصُّدُورِ

Aka bayyana abin da ke cikin zukata

Ayah 10

إِنَّ رَبَّهُم بِهِمۡ يَوۡمَئِذࣲ لَّخَبِيرُۢ

Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne

Ayah 11